Har ila yau wata kafar yada labarai ta kasar England ta ba da labarin cewa, Louis van Gaal ya cimma matsaya daya da kulob din Manchester, kuma babu shakka zai jagoranci kulaf din a kakar wasa mai zuwa. Haka nan an ba da labarin cewa, Louis van Gaal ya cimma matsaya da kulaf din cewa, ba zai shigo da dukkan mambobin tawagar sa ta baya ba, inda maimakon hakan ya bayyana niyyarsa ta shigo da Ryan Giggs cikin kungiyar tasa. A nasa bangare, Ryan Giggs ya nuna cewa, yana fatan ci gaba da koyon fasahar horas da 'yan wasa tare da Louis van Gaal.
Koda yake wasu na ganin Ryan Giggs bai nuna kwarewa sosai ba bisa matsayinsa na mai ba da taimako ga Louis van Gaal, amma kasancewar sa kwararren dan wasan Manchester, Ryan Giggs zai bai da taimako wajen karfafa hulda tsakanin Louis van Gaal da 'yan wasan kungiyar. Kuma van Gaal na iya yin shawarwari da Ryan Giggs, wajen yanke shawarwari kan 'yan wasan kungiyar da za su buga wasanni masu zuwa.
Wata kafar yada labaru ta England dai ta taba bayyana cewa, Ryan Giggs bai yi ritaya ba tukuna, kuma ana aza ayar tambaya kan ko Ryan Giggs zai kasance dan wasan kwallon kafa kuma mamba cikin tawagar horas da 'yan wasa, ko kuma mai ba da taimako ga babban mai horas da kungiyar kadai. (Amina)