in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kocin Stuttgart ya yi sallama da kulaf din
2014-05-14 16:37:47 cri
Kocin kulaf din Stuttgart na kasar Jamus Huub Stevens ya yi sallama da kulaf din, bayan da Stuttgart din ya tsallake faduwa kasa warwas.

Kulaf din na Stuttgart dai ya kammala kakar wasanni ta bana a matsayi na 15 da jimillar maki 32, aikin da shi kan sa Stevens ya bayyana da mai matukar wahalar gaske. Stevens dai ya karbi aikin horas da kulaf din na Stuttgart ne a watan Maris, aikin da acewar sa bai wuce na hana kulaf din fadowa matsayin fita daga rukunin kulaflikan dake ajin kwararrun kasar ba. Yace yanzu haka ya yanke shawara tare da iyalinsa game da barin kungiyar. Koda yake ya ce Stuttgart na wani matsayi da zai bata damar kasancewa, a wani sashen mai muhimmanci a teburin gasar da za a fara ta kakar wasanni mai zuwa.

A hannu guda kuma jagoran kulaf din na Stuttgart Bernd Wahler ya bayyana cewa, sun fahimci ma'anar shawarar da Stevens ya yanke, kuma suna godiya gare shi game da gudummawar da ya baiwa kulaf din na su. Gudummawar da ta fidda kulaf din daga fadawa mawuyacin hali, a cewar Bernd Wahler.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China