Yayin da ake aikin gwajin filin, masu kallo dubu 20 sun shiga cikin sa, wanda bisa tsari zai iya daukar 'yan kallo dubu 65. Wanda kuma bayan nazari a wannan karo na biyu, aka gano cewa akwai wasu matsaloli a tattare da filin. Babbar matsalar da aka gano dai ita ce batun sadarwa. Inda babu wata waya dake iya shiga ko fita daga filin, balle shiga yanar gizo ta hanyar amfani da wayar salula.
A cewar jami'i mai kula da wannan filin wasa, har yanzu ba a kammala kafa tsarin sadarwa na WIFI a filin wasan ba, ko da yake ya jaddada cewa ba a filin wasan Etta Gellar kawai aka gamu da irin wannan matsala ba.
Baya ga wannan, yayin da 'yan kallo suke shiga filin wasan, ba sa iya tantance daidaitacciyar hanya. Wato dai ana shan fama wajen gane hanyoyin shiga filin, yayin da wasu ma'aikata marasa hakuri kewa 'yan kallon tsawa, maimakon nuna musu hanyar da ta dace su bi.
Bugu da kari akwai batun wata zanga-zangar da aka yi a birnin Rio de Janeiro, wanda hakan ya yi babbar barazana ga batun tsaron al'umma a yayin gasar ta cin kofin duniya.
Kaza lika a ranar 8 ga wata, wasu direbobin bas-bas sun yi yajin aiki a birnin, domin nuna bukatarsu ta neman karin albashin kaso 40. Lamarin da ya janyo lalata motoci sama da 300, yayin da wasu suka cinna wuta kan wasu motocin. Kuma ko da yake mataimakin shugaban kungiyar 'yan kwadago ta direbobin bas din ya bayyana cewa, yawan bas din da suka daina aiki basu wuce kashi 20 cikin dari ba, a hannu guda zanga-zangar ta kawo babbar illa ga harkokin sufuri a cikin birnin. Kuma an rufe makarantu da kamfanoni da yawa, yayin da aka kuma samu cunkoson motoci kan hanyoyin birnin.
Dadin dadawa, a ranar 7 ga wata, a birnin dai na Rio de Janeiro, kimanin 'yan sanda 50 sun gudanar da zanga-zangar lumana, a harabar filin gabatar da jerin sunayen 'yan wasan kwallon kafa na kungiyar Brazil, wadanda za su shiga gasar cin kofin na duniya a bana, inda 'yan sanda suka yi barazanar cewa, idan ba a kara musu albashi ba, za su yi yajin aiki a yayin gasar dake tafe.
Bisa alkaluman da hukumar yawon shakatawa ta birnin Rio de Janeiro ta gabatar, an yi kiyasin cewa, masu yawon shakatawa kimanin dubu 600 za su ziyarci kasar ta Brazil, a yayin gasar cin kofin na duniya, kuma a cikinsu kashi biyu bisa uku za su ziyarci birnin na Rio de Janeiro.
Za dai a gudanar da wasanni 7 a wannan birni, ciki har da wasan karshe. Yayin da a gefe guda ake ci gaba da fama da matsalolin tsaro a sakamakon yawaitar zanga-zangar da ake yi.
A wani ci gaban kuma, gwamnatin jihar Mato Grosso ta kasar Brazil ta sanar a ranar 8 ga wata cewa, an samu aukuwar wani mummunan hadari a filin wasan kwallon kafa na Arena Pantanal, wanda aka gina shi domin gudanar da gasar ta bana. Hadarin da ya yi sanadiyyar mutuwar wani ma'aikaci mai shekaru 32.(Fatimah)