Rahotanni dai sun bayyana cewa shugaban hukumar ta FKF Sam Nyamweya ne ya ba da wannan umarni a ranar Alhamis. Biyowa bayan dakatar da shi da babban kocin kasar Adel Amrouche dan kasar Belgium ya yi daga aikin sa, bisa zargin kauracewa aiki ba bisa ka'ida ba, yayin da aka dorawa Nandwa nauyin lura da kulaf din matasa na kasar wato AFC Leopards.
Wannan dai mataki da hukumar ta FKF ta dauka zai sanya Nandwa kasancewa cikin tawagar kungiyar ta Harambee stars, wadda za ta shiga gasar cin kofin zakarun nahiyar Afirka da AFCON ke shiryawa a shekarar 2015 mai zuwa. Inda kulaf din zai buga wasan share fagen zagayen farko na gasar da kulaf din kasar Comoros a ranar 18 ga watan nan na Mayu a birnin Nairobin kasar Kenya.
Bisa sabon matakin da hukumar FKF ta dauka, ana sa ran James Nandwa zai koma sansanin horas da 'yan wasan kungiyar dake Nairobi, zai kuma ci gaba da kasancewa mataimaki ga koci Amrouche. A cewar jagoran hukumar FKF, ba za su maida hankali ga jita-jita game da korar wancan jami'in horas da 'yan wasa ba, maimakon haka za su tunkari shirye-shiryen gasar ta AFCON dake gabansu yadda ya kamata.
Ya ce FKF ce kadai ke da alhakin kora, ko nada mai horas da 'yan wasa, kuma aikin ta ne ta yi kokarin ganin an horas da masu horas da 'yan wasa na gida, aikin da kuma a cewarsa ba zasu yi wasa da shi ba. Kaza lika Nyamweya ya bayyana aniyar su ta sake nemo wani kwararren jami'in horas da 'yan wasa, wanda zai taimakawa kwarewar 'yan wasan kasar.