in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An rufe babban taron yanayin Warsaw
2013-11-24 17:18:24 cri
A daren ranar Asabar 23 ga wata, an kammala taron tsakanin wakilan da suka daddale yarjejeniyar tinkarar sauyin yanayin MDD da takardar Kyoto bayan cimma matsaya tsakaninsu a birnin Warsaw na kasar Poland.

Ko da yake ba a biya duk bukatun da kasashe masu tasowa suka bayar ba, amma tawagar Sin ta bayyana cewa, kome irin ci gaban da za a samu, Sin za ta tsaya tsayin daka kan bin hanyar neman samun bunkasuwa ba tare da gurbata muhalli ba.

Ban da haka, tawagar Sin ta kara da cewa, a gun wannan taro, an yanke shawara ta karshe kan batutuwa uku da kowa ke mai da hankali a kai, wato yunkurin dandalin Durban, tsarin biyan diyya, da kuma batun kudi, wadanda aka cimma matsaya a kai.

An bude wannan taro a ranar 11 ga wata, kuma an yi shirin kammala shi a ranar 22 ga wata. Amma sabo da babban gibin dake tsakanin kasashe masu sukuni da kasashe masu tasowa kan manyan ka'idojin tinkarar sauyawar yanayi, tsarin ba da diyya, batun kudi da sauransu, shi ya sa an ci gaba da yin shawarwari har zuwa daren ranar 23 ga wata. (Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China