A ran 17 ga wata, kotun koli ta Kamaru ta bayar da sakamakon zaben majalisar dokoki da na kananan hukumomin kasar da aka yi ranar 30 ga wata, bisa sakamakon da aka bayar, an ce, jam'iyyar da ke kan karagar mulki a kasar ta Kamaru wato Jam'iyyar R.D.P.C ta sake samun nasara mai rinjaye, inda ta samu kujeru 148 daga cikin 180 na majalisar dokokin kasar, kana ta 'yan adawa a yawancin biranen kasar, ta yadda za ta ci gaba da jagorantar harkokin siyasar Kamaru.
Akwai sama da jam'iyyun siyasa 250 da aka yiwa rajista a kasar ta Kamaru, inda jam'iyyu 29 daga cikinsu suka shiga zaben majalisar dokokin kasar da aka yi. Babbar jam'iyyar adawa ta farko wato Jam'iyyar 'Social Democratic Front' ta samu kujeru 18, inda ta kara samun kujeru biyu idan aka kwatanta yawan kujerun da ta samu a karon da ya gabata, sauran jam'iyyun adawa guda 4 su ma sun samu kujeru kadan. A cikin birane da yawansu ya kai 360 da aka gudanar zaben kananan hukumomin kasar, dan takarar Jam'iyyar R.D.P.C ya samu dukkannin ko yawancin kujeru a birane 305.
Bisa kundin tsarin mulkin Kamaru, an ce, za a shirya zababbun majalisar dokoki dana birane ne a ko wadanne shekaru 5. Bisa shirin da aka tsara a da, ya kamata a shirya zababbun wannan karo a shekarar da ta gabata, amma aka dage zuwa shekara ta 2013 sakamakon rajistar masu jafe kuri'u bisa fasahohin zamani don daukar hotunan yatsunsu, da kuma tsawon lokacin da ake dauka wajen yin katin masu jefa kuri'u.(Danladi)