in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kai hari kan wani kamfanin kasar Sin dake Kamaru
2014-05-17 20:45:22 cri
Ofishin jakadancin kasar Sin dake kasar Kamaru ya shaida a yau ranar Asabar cewa, wasu dakarun da ba a san asalinsu ba sun kai hari kan wani reshen kamfanin mai kula da aikin gina kayayyakin more rayuwa na kasar Sin da ke jihar Extrême-Nord a kasar Kamaru a daren jiya 16 ga wata, lamarin da ya yi sanadiyyar jikkatar wani ma'aikacin kasar Sin dake wurin, yayin da wasu goma suka bace ba a san inda suke ba, haka zalika maharan sun yi awon gaba da motoci 10.

Ofishin jakadancin kasar Sin dake Kamaru ya riga ya dauki matakan gaggawa, da kuma aike da wasu jami'ai a wurin da lamarin ya faru. Kuma tuni Ofishin jakadancin kasar Sin ya kalubalanci bangaren Kamaru da ya dauki matakan da suka dace, don gudanar da ayyukan ceto, wanda zai ba da tabbaci ga tsaron ma'aikatan Sin da gano wadanda suka bace, da ma bada kula ga sauran ma'aikatan dake wannan yanki na Extrême-Nord.

Har zuwa yanzu babu wata kungiyar da ta dauki alhakin wannan lamarin. (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China