Za'a gina wata hanya mai tsawon kilomita 312 da zata hada kasashen Congo da Kamaru
Jamhuriyar Congo-Brazzaville za ta kaddamar a cikin watan Maris wasu ayyukan da suka shafi gina wata doguwar hanya mai tsawon kilomita 312 a Ouesso dake kuryar arewacin kasar da zata kai har zuwa kasar Kamaru a wani labarin da ya fito daga bakin ministan gine ginen kasar Congo a ranar Talata. Hanyar Ketta-Djoum-SongMelina wani aiki ne da ya samu tallafin kudi daga bankin cigaban kasashen Afrika (BAD) da gwamnatin Congo duk da cewa ba'a fayyace adadin kudin har yanzu ba.
Jamhuriyar Congo ta dauki niyyar warware matsalarta a matsayin kasar da ake ratsawa ta wannan yanki na tsakiyar Afrika. Tun a shekarar 2011, gwamnatin kasar ta aiwatar da wani babban tsari na gina hanyoyin da za su hade da manyan biranen kasashen dake makwabtaka da kasar kamar kasashen Kamaru, Gabon, Cadi zuwa Afrika ta Tsakiya.
Bisa wannan manufa, shugaban kasar Sassou-Nguesso ya kaddamar a cikin watan Nuwamban shekarar 2011 wasu ayyukan gina hanyar da za ta tashi daga Congo zuwa Gabon, daga yankin Okoyo-Lekety-Lekoni a kan iyakar Gabon. (Maman Ada)