in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Kamaru na neman sake bunkasa tsarin wasan hannu na volley-ball a cikin makarantun kasar
2011-12-22 14:32:03 cri
Kasar Kamaru zata sake bunkasa tsarin wasan hannu na volley-ball, wannan kuma tun cikin watan Janairu mai zuwa a cikin makarantun jihohi goma na kasar domin baiwa 'yan makaranta masu shekaru takwas zuwa goma damar samun horo da kwarewa kan wasan motsa jiki a wani labari da hukumomin kasar suka bayar a ranar Laraba.

"tsarin bunkasa harkar wasan volley-ball a makaranta wata makoma ce mai kyau ta bunkasa wasan hannun volley-ball a Kamaru. Yana daya daga cikin manyan tsare tsare na kungiyarmu har zuwa wasannin Olympic biyu da za'a shirya a nan gaba. Muna bukatar horar da matasa 800 har zuwa shekarar 2020", in ji shugaban kungiyar Kamaru ta wasan volley-ball (FCVB), mista Majore Louis Timba a yayin da yake hirawa da kamfanin dillancin labarai na Xinhua.

Wannan tsari, wata babbar hanya ce ta "gano, zabo da shirya 'yan wasan da za su iyar gogawa da manyan 'yan wasa na duniya a cikin rukunin matasa da yara kanana a matakai daban daban, bada horon gaba daya ga 'yan wasa da bunkasa wasan volley-ball a duk fadin kasar'.

Tsarin bunkasa wasan hannu na volley-ball a kasar Kamaru an kirkiro shi tun a shekarar 2006, sai dai kuma aka kasa fara aiwatar da wannan tsari dalilin rashin kudi. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China