A jawabinsa na rufe taron, sabon shugaban kungiyar na wannan karo kana shugaban kasar Mauritaniya, Mohammed Ould Abdel-Aziz ya ce, nahiyar tana sane da tarin nauyi da kalubalen da ke gabanta kafin ta kai ga turbar samun bunkasuwa, kuma za ta himmatu wajen ganin ta tunkari wannan jan aiki da ke gabanta.
Ya ce, muna son gina nahiya mai makoma mai haske, tsarin demokiradiya kana nahiya mai kishin al'ummar ta wadda kuma za ta iya magance matsalolinta da kanta.
Bugu da kari, sabon shugaban kungiyar ya ce bisa la'akari da yadda galibin kasashen nahiyar ke fama da tashin hankali, shugaban ya jaddada bukatar hanzarta kafa rundunar nahiyar da za ta rika magance tashe-tashen hankulan da suka kunno kai a nahiyar, tare da karfafa wa kasashe mambobin kungiyar, da su bayar da gudummawar dakaru.
Daga karshe, ya sake yin kira ga kasashen nahiyar da su rika magana da murya guda game da batutuwan kasa da kasa, kamar harkokin cinikayya da matsalar canjin yanayi. (Ibrahim)