Kungiyar AU ta yi maraba da cigaban da aka samu na samar da zaman lafiya a Sudan ta kudu
Shugaban kwamitin Kungiyar Tarayyar kasashen Afrika AU Madam Nkosazana Dlamini-Zuma tayi maraba da cigaban da aka samu a kokarin samar da zaman lafiya a kasar Sudan ta kudu,bayan makwanni biyu da aka yi ana ta tattaunawa akan cimma matsaya da tsarin da za'a bi a siyasance domin samar da sulhu da kuma waraka abin da ake fuskanta.
Madam Nkosazana Zuma ta yaba matuka ga wakilan musamman na kungiyar raya gwamnatocin gabashin Afrika IGAD wadanda sune suka yi ta shiga tsakani wajen tattaunawa tsakanin bangarorin biyu na kasar Sudan ta kudun, a cewar ta kokarin wadannan masu shiga tsakanin ne ya sa aka samu dawo da tattaunawa aka kuma kai inda ake a yanzu.(Fatimah Jibril)