Wannan dai mataki ya yi daidai da bukatar kungiyar habaka tattalin arzikin yankin tsakiyar nahiyar Afirka ECCAS, kungiyar da a taronta da ya gabata a birnin N'Djamena na kasar Chadi, ta amince da kafa wata majalissar da za ta zamo tambar majalissar dokokin rikon kwarya, a tsawon lokacin da ba zai zarta watanni 18 ba, wato gabanin gudanar zaben da zai fidda sabon shugaban kasar bisa tsari irin na Dimokaradiyya.
Tuni dai ECCAS ta yi Allah wadai da juyin mulkin kasar ta Afirka ta tsakiya, tana mai yin tir da matakin da Djotodia ya dauka, na nada kansa shugaban kasa, tare da bukatarsa da ya martaba yarjejeniyar sulhu da aka cimma a birnin Libreville cikin watan Janairun da ya gabata.
Sabuwar majalissar da aka kafa dai a wannan kasa, na kunshe da mambobi 97, da suka hada da mutane 10 daga rundunar 'yan tawayen Seleka, da kuma wasu 20 daga ragowar jam'iyyun siyasar kasar, sai kuma ragowar da suka fito daga sassan jagororin al'umma da masu fada a ji.
Kafin dai hakan Djotodia, wanda ya haye karagar mulkin kasar bayan hambarar da shugaba Francois Bozize daga gadon mulki, a ranar 24 ga watan Maris daya gabata, ya ambata cewa, zai jagoranci kasar ne har tsawon shekaru 3 masu zuwa, karkashin dokoki irin na soji, kafin mika mulki ga zababbiyar gwamnati, kudurin da ga alama, bai samu amincewar masu ruwa da tsaki ba.(Saminu)