A cikin wata sanarwa da kwamitin ya fitar, an nuna cewa yana nuna matukar damuwa game da ayyukan kungiyoyin ta'addanci da suka hada da Al-Qa'ida na yankin Maghreb da MUJIAO tare da yin tir da kakkausar murya akan harin kwanan nan.
Kwamitin ya kuma bayyana damuwa akan yaduwar makamai, yawan fadace fadace da muggan makamai, yawan fataucin miyagun kwayoyi da duk wassu laifuffuka da ake aiwatar da basu dace ba dake da alaka da ta'addanci.
Haka kuma kwamitin ya yi kira ga yankin Sahel, yammacin Afrika da kasashen Maghreb da su samar da dabaru masu inganci da zai magance ayyukan ta'addanci da laifuffukan da aka tsara su domin hana yaduwar makamai. Sannan kuma in ji sanarwar, kwamitin ya jaddada muhimmancin samar da bayanai da kuma hadin kai tsakanin MDD, cibiyar magance ta'addanci ta duniya, kungiyar tarayyar kasashen Afrika AU, da sauran wassu kungiyoyi masu ruwa da tsaki. (Fatimah)