Kwamitin tsaron MDD ya bukaci da a samar da sahihin tsarin yaki da ta'addanci, duba da cewa, ba zai yiwu a kau da ayyukan ta'addancin a fadin duniya ta hanyar amfani da karfin soji ko ta ragowar hanyoyin tsaro kawai ba. Kwamitin tsaron mai wakilcin kasashe 15 ya fitar da wata sanarwa a karshen zaman mahawara na yini guda da ya gudana ranar Talata 15 ga wata, wadda ke bayyana bukatar da ake da ita, ta magance dalilan yaduwar ayyukan ta'addanci a sassan duniya.
Kwamitin ya kara da cewa, ana iya shawo kan wannan matsala ne kawai, idan dukkanin kasashe da hukumomi masu ruwa da tsaki suka hada kai da juna, wajen daukar matakan dakile kalubalen da ta'addancin ke haifarwa.
A wannan karo, kasar Pakistan dake rike da shugabancin kwamitin na karba-karba ce ta jagoranci zaman mahawarar. Ya kuma zo daidai lokacin da kasar ke fuskantar barazanar ayyukan ta'addanci da dama, inda cikin makon da ya gabata ta fuskanci hare-haren kunar bakin wake guda 4 a jere. Uku daga hare-haren an kaddamar da su ne a Quetta, babban birnin lardin Balochistan dake kudu maso yammacin kasar, mai iyaka da kasashen Afganistan da Iran. Yayin da guda 1 ya auku a wata cibiyar wa'azi dake yankin arewa maso yammacin Swat.(Saminu)