A ran 27 ga wata, manyan kamfanoni uku na hakar ma'adinai na Platinum na kasar Afirka ta Kudu wato kamfanin 'Anglo- American Platinum' da na 'Impala Platinum' da na 'Lonmin Platinum' sun yi shawarwari da kungiyar ma'aikatan hakar ma'adinai da kungiyar kwadago ta gine-gine.
Bisa rahotannin da aka samar an ce shawarwarin tsakanin wadannan kamfanoni da ma'aikata sun shiga cikin halin ja-in-ja, kuma har zuwa yanzu ma'aikata masu hakar ma'adinnai dubu 80 suna cigaba da yajin aiki.
A halin yanzu, bangarorin biyu ba su cimma matsaya game da albashin ma'aikata ba, dukkan bangarorin biyu ba su son yin sassauci daga matsayin su, sabo da haka shawarwarin da ake yana cikin mawuyacin hali. Shawarwarin da aka yi a wannan rana ba shi da wani matsayi mai muhimmanci, ganin yadda manyan shugabanni da manajojin kamfanonin uku da shugabannin kungiyoyin kwadago ba su halarta ba.
A yayin da ake shawarwari, ana ci gaba da yajin aiki, sai dai ba wani tashin hankali. Sakamakon yajin aikin da ake yi, darajar kudin Afirka ta Kudu Rand kan Dalar Amurka na ranar 27 ga wata ya yi kasa sosai, har ma ana canza Rand 11.25 a kwatankwacin dalar Amurka guda.(Danladi)