A 'yan kwanakin baya, mutane 9 sun mutu sakamakon tsawa a rana daya a jihar Mpumalanga da ke arewacin kasar Afirka ta Kudu. Shugaban kasar Jacob Zuma ya nuna ta'aziyya ga wadanda suka mutu, kuma ya yi kira ga jama'a da su kara tsaron kansu yayin zuwan damina.
Kasar Afirka ta Kudu tana kasancewa daya daga cikin kasashen da suke fi shan wahala daga bala'un tsawa, daga watan Oktoba zuwa watan Maris na shekara mai zuwa yanayin damina ne, tsawa take zuwa a kusan ko wace rana. Bisa kididdigar da hukumar lura da yanayi ta Afirka ta Kudu ta bayar, an ce, a wace shekara yawan mutanen da suka mutu sabo da tsawa ya zarce 260 a duk fadin kasar.
Kwararrun yanayi sun yi nazari cewa, a 'yan shekarun baya, yawan jama'ar da suka mutu ko raunata sakamakon tsawa na karuwa, ban da tunani maras karfi da jama'a suke da shi wajen tsaron kansu daga bala'un tsawa, sauyawar yanayi ta zama wani muhimmin dalilin da ya sa aka kara samun irin wannan hadari.(Danladi)