Malam Salissou wanda ya halarci babban taron zuba jari kan kayayyakin more rayuwa na Macao karo na biyu da aka yi nan birnin Beijing, a lokacin zantawarsa da wakilin Gidan Rediyon CRI na musamman, ya bayyana cewa, a halin yanzu, kasar Sin na dukufa wajen cimma burinta, don haka kasar Nijer ita kuma tana kokarin wajen cimma nata burin na shirin raya tattalin arziki tsakanin shekarar 2012 da ta 2015, da kuma shirin samar da isassun abinci da kanta.
A cewar ministan yana fatan tsarin hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Afirka da firaministan Li Keqiang ya bayyana zai iya taimakawa kasashen biyu wajen cimma burinsu tare. (Maryam)