in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Jamhuriyar Nijer ya gana da babban jami'in Sin Mista Wang Jiarui
2014-01-13 10:43:05 cri

A ran 11 ga wata a Yamai, babban birnin Jamhuriyar Nijer, shugaban kasar Mahamadou Issoufou ya gana da Mista Wang Jiarui, mataimakin shugaban majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin, kuma shugaban sashen kula da harkokin cudanya da ketare na kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, wanda ya kai ziyara kasar Nijer.

Wang Jiarui ya isar da gaisuwar shugaban Sin Xi Jinping zuwa ga shugaba Issoufou, inda ya ce, Sin tana mai da hankali kan dangantakar da ke tsakanin Sin da Nijer, kuma tana son kara ciyar da dangantakar Sin da Nijer gaba. JKS tana son kara cudanya da Jam'iyyar PNDS-Tarayya, don yin musanyar ra'ayi wajen tafiyar da harkokin kasashen biyu.

A nasa bangare, Mahamadou Issoufou ya nuna cewa, Nijer tana darajanta dangantakar da ke tsakanin jam'iyyun biyu da kasashen biyu, hadin kai a tsakanin kasashen biyu na da kyakkywar makoma, Nijer ta nuna yabo ga sabon ra'ayin Sin na samun moriyar juna da nasara tare, kuma tana maraba ga kamfanoni da masu zuba jari na kasar da su kara shiga cikin bunkasuwar tattalin arziki da zaman al'ummar Jamhuriyar Nijer.(Danladi)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China