in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kamfanin kasar Sin CCECC da gwamnatin Nijeriya sun daddale yarjejeniyar gina hanyoyin jiragen kasa da ke dab da teku
2014-05-06 15:48:49 cri

Kamfanin gine-gine na kasar Sin wato CCECC da ma'aikatar zirga-zirga ta Nijeriya sun daddale yarjejeniyar gina hanyoyin jiragen kasa da ke dab da teku a ranar 5 ga wata a birnin Abuja, babban birnin tarayyar Nijeriya.

Shugaban kamfanin CCECC Mista Liu Zhiming da ministan zirga-zirgar Nijeriya Abdullahi Umar ne suka sanya hannu kan yarjejeniyar. Wannan dai ya shaida cewa, kasar Sin ta samu sabon ci gaba wajen fitar da ma'aunanta na gina hanyoyin jiragen kara zuwa kasashen ketare.

Wannan hanyar jiragen kasa da za a gina za ta ratsa jihohi goma, tare da yankin hakar man fetur da ke yankin Niger Delta. Kuma tsawonta zai kai kilomita 1,385. Jiragen kasa za su yi tafiyar kilomita 120 a ko wace sa'a, kan wannan sabon layin dogo, da za a kafa tashoshi 22 a kansa.

Wannan aikin gina hanyar jiragen kasa da ke dab da teku ya kasance wani muhimmin sashe na zirga-zirgar hanyoyin jiragen kasa da ke hada kasa da kasa na kungiyar ECOWAS, bayan kammalar aikin, zai kasance mai muhimmanci matuka wajen sa kaimi ga bunkasuwar tattalin arziki a yammacin Afirka, da raya tattalin arziki a yankunan da ke dab da teku. (Danladi)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China