in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Nijar ta cimma wasu sabbin matakai na hakar ma'adinan kasar
2013-12-29 16:10:20 cri
Gwamantin kasar Nijar ta cimma wasu sabbin matakan da suka shafi aiwatar da dokar dake nasaba da hakar ma'adinan kasar, a cewar wani sakamakon zaman taron ministocin kasar da ya gudana a ranar Jumma'a, lasin yin bincike da kuma lasin hakar ma'adinai sun kasance na dogaro da yarjejeniyar ma'adinai da gwamnati za ta sanya hannu nan gaba tare da wanda ko wadanda suka samu wadannan lasisi daga lokacin da suka same su.

A cewar sabbin matakan da wannan sabon kudurin da gwamnatin Nijar ta sanya ma hannu sun nuna cewa yarjejeniyoyin da aka sanya ma hannu a baya za su ci gaba da aiki har sai lokacin karshen wa'adinsu. Sabon kudurin na yanzu ya kawo gyaran fuska da kuma kari bisa ga na tsohon kudurin da aka dauka a shekarar 2006. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China