Ganawar tsakanin wadannan manyan jami'ai biyu ta taimaka wajen yin tilawar muhimman batutuwan dake ciwa yankunan na Afrika tuwo a kwarya, musamman ma matsalolin tsaro da ake fuskanta a kasashen Sahel da kasar Libiya.
Ya tabbatar da kusancin ra'ayoyinmu da kuma amincewa da juna dake tasiri a cikin dangantakarmu, in ji kakakin fadar Quai d'Orsay.
Musamman ma, mista Fabius ya nuna babban yabo kan kokarin da kasar Nijar take yi wajen tabbatar da zaman lafiya a yankin Sahel, in ji kakakin. (Maman Ada)