in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Benin ta lashe gasar kwallon kafar yammacin Afirka ta matasa 'yan kasa da shekaru 17
2014-05-06 15:37:17 cri
Kulaf din kasar Benin ya lashe gasar kwallon kafar yankin yammacin Afirka ta matasa 'yan kasa da shekaru 17 ta WAFU, wadda aka buga tsakanin ranekun 19 zuwa 27 ga watan Afirilun da ya gabata, a birnin Lome na kasar Togo.

A wasan karshe "yan wasan kungiyar ta Benin sun doke takwarar su ta Mali da ci 2 da 1, bayan tsallakawa karin lokaci, bayan da aka tashi wasan 1 da 1. Matakin da ya basu zarafin daukar kofin da aka yi wa lakabi da 'President Cup'.

Wannan gasa dai ta zamo tamkar share fage ce ga kungiyoyin dake shirin shiga zagayen farko na gasar kwallon nahiyar Afirka, ta 'yan kasa da shekaru 17, wadda za a buga a kasar Niger cikin shekarar 2015 mai zuwa.

Kafin daukar kofin sai da 'yan wasan na Benin suka taka leda da 'yan wasan Togo, wadanda suka doke Benin din da ci 2-1, su kuma 'yan Benin din suka rama kan Cote d'Ivoire da ci 2-1, kafin su fitar da Nigeria da ci 3-1, a zagayen kusa da na karshe, ta hanyar bugun daga kai sai mai tsaron gida.

Golden Eaglets na Najeriyar ne dai ya zamo na uku da lambar tagulla, bayan ya doke Togo a wasan neman zama na uku. Haka kuma dan wasan gaban Benin Aaron Ibilola ya samu lambar yabo, ta dan wasa mafi yawan kwallaye a gasar bayan da ya sanya kwallaye 3 a raga, sai kuma Mohamed Hairdara na Mali da aka zaba dan wasa mafi hazaka a daukacin gasar.

Bisa jimilla an buga wasanni 9 a wannan gasa ta WAFU.

Inda a rukumin farko na A aka fara da wasan

19/Afirilun/2014 Togo 2-1 Benin.

21/04/2014 Benin 2-1 Cote d'Ivoire.

23/04/2014 Cote d'Ivoire 1-1 Togo.

Sai kuma wasannin rukuni na Biyu na B

19/04/2014 Mali 0-2 Nigeria.

23/04/2014 Nigeria 2-0 Mali.

A wasannin zagayen kusa da na karshe kuwa

25/04/2014 Nigeria 1-1 (kafin bugun daga kai sai mai tsaron gida da aka yi, aka kuma tashi Benin na da 3, Najeriya na da 1.

Akwai kuma wasan neman na Uku da Najeriya ta lashe Togo da ci 3-0.

Kafin kuma a buga wasan karshe, wanda Benin ta lallasa Mali da ci 2-1.

Bugu da kari baya ga daukar kofin gasar da Benin ta yi, an zabi Najeriya a matsayin kulaf mafi da'a. An kuma zabi mai tsaron gidan Najeriya Benjamin Amos a matsayin mai tsaron gida mafi kwarewa a gasar.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China