in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Tsohon dan wasan dambe Rubin Carter ya rasu sakamakon cutar Cancer
2014-05-01 17:24:28 cri

Tsohon shahararren dan wasan damben kasar Amurka bakar fata Rubin Carter ya rasu da safiyar ranar 20 ga watan Afrilu, ya na da shekaru 76 da haihuwa. Carter ya rasu ne a gidansa dake birnin Toronton kasar Canada bayan ya sha fama da cutar daji ko Cancer.

An haifi Rubin Carter ne dai a Clifton dake jihar New Jersey ta kasar Amurka a shekarar 1937. Kuma ya fara shiga gasar dambe ta Amurka a shekarar 1961. Ko da yake Carter ba shi da tsayi sosai, amma yana da kwarewa sosai wajen wasan dambe. Inda a cikin shekaru 5 ya samu nasarar lashe wasanni har sau 27 a gasannin da ya shiga. A sabili da haka ne ake yi masa lakabi da "guguwar iska".

A shekarar 1993, hukumar dambe ta duniya ta ba shi kambi na zinariya, wadda ta tabbatar da shi a matsayin gwanin dambe a matsayi na matsakaita, daga bisani kuma aka shigar da Carter cikin kungiyar shahararrun 'yan wasan dambe ta jihar New Jersey.

Rayuwar wannan dan wasan dambe ta sauya a shekarar 1966, bayan da aka zarge shi da aikata laifin kisan kai, aka kuma yanke masa hukunci daurin rai da rai. Kafin daga bisani a shekarar 1985, a gano cewa bai aikata wannan laifin da aka zarge shi da aikatawa ba. Bayan fitar sa daga kurkuku kuma Carter ya yi kaura zuwa birnin Toronto.

Kamfanin dillancin labaru na AP ya bayyana cewa, batun rashin adalci da aka yiwa Carter ya ja hankalin duniya, wajen nuna bambancin launin fata da aka rika nunawa wasu al'ummu a Amurka. Inda har ta kai ga a shekarar 1966, 'yan sanda sun cafke Carter da abokinsa John Artiles, suka tuhume su da aikata laifin harbe wasu mutane biyu da mace daya a jihar New Jersey. Ko da yake ba a samu cikakkun shaidu masu ganewa ba game da faruwar wannan laifi, amma alkali ya yanke musu hukuncin aikata laifin, a shekarar 1967 da shekarar 1976, daga bisani aka yanke wa Carter hukunci daurin rai da rai.

Cikin irin wannan yanayi na rashin adalci, Carter ya kammala rubutunsa mai suna "Zagaye na 16" dangane da tarihin rayuwar sa a gidan yari. Aka kuma gabatar da wannan littafi a shekarar 1975, matakin da ya jawo hankalin jama'a, da samar masa goyon baya sosai. Har ta kai ga shahararren mawakin Amurka, Bob Dylan ya kai masa ziyara a gidan kurkuku a wannan shekara. Daga bisani ya fitar da wata waka mai suna "Guguwar iska"ta tsawon minti 8, domin nuna goyon baya ga Carter.

Bayan da Carter ya yi shekaru kusan 20 yana zama karkashin zargin da aka yi masa, wato a shekarar 1985, kotun tarayyar Amurka ta sake duba hukuncin da aka yankewa Carter, bisa bambancin launin fata, a maimakon hakikanin abubuwan da suka faru. A sabili da haka, sabon hukuncin ya nuna cewa Carter bai aikata laifin da aka zarge shi da aikatawa ba, aka kuma sake shi nan take.

A shekarar 1999, an shirya wani fim mai suna "Guguwar iska" bisa labarin rayuwar Carter, inda shahararren jarumin fim din nan dan kasar Amurka Denzel Washington ya fito a matsayin Carter.(Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China