140508-mai-tsaron-gidan-najeriya-enyeama-na-jerin-yan-takarar-babbar-lambar-yabo-ta-kwararru-bello
|
Mai tsaron gidan kulaf din kwallon kafan Super Eagle ta Najeriya Vincent Enyeama, ya shiga jerin 'yan takarar babbar lambar karramawa, ta kwararrun 'yan wasa, da kungiyar kwararrun 'yan kwallon kafar kasar Faransa UNFP ke bayarwa.
Ragowar 'yan wasan dake takarar wannan lambar yabo sun hada da dan Faransa Steve Mandanda, dake bugawa kulaf din Olympique Marseille wasa, akwai kuma Salvatore Sirigu mai tsaron gidan PSG dan asalin kasar Italiya, sai kuma Stephane Ruffier na Saint-Ettiene.
Enyeama, dan shekaru 31, ya baiwa kulaf din sa na Lille OSC kariya mai yawa a kakar wasa ta bana, inda ya kare kwallaye kwarara 21. Yayin da kuma aka zura masa kwallaye 21 a wasanni 35 da ya tsarewa kulaf din na sa gida. Matsayin da ya sanya shi kasancewa na biyu bayan mai tsaron gida Sirigu na PSG, a jerin masu tsaron gida mafiya hazaka.
Yanzu dai haka Lille na matsayi na 3, gabanin wasanni 3 da suka ragewa kulaf din. Kuma muddin kulaf din ya tsare matsayin sa na yanzu, zai kai ga samun zarafin shiga kungiyoyin kwallo, da za su shiga zagayen farko na gasar cin kofin zakarun turai a kakar wasanni mai zuwa.
Rahotanni dai na cewa za a gabatar da bikin mika lambar yabon ne ga dan wasan da ya yi nasara ran 11 ga watan nan na Mayu, mako guda kafin kammala gasar kakar wasan kasar ta Faransa ta bana.