Masu zanga-zanga fiye da dubu 10, wadanda suka tashi daga wasu lardunan dake kudancin kasar, sun kwashe kwanaki 4 suna tafiya har suka kai birnin Sana'a a ranar 24 ga wata, inda suka gabatar da koke-koken rashin yarda da yadda aka baiwa shugaban kasar Ali Saleh kariya daga tuhumar aikata laifi. Daga bisani, rikici ya barke a tsakanin masu zanga-zangar da sojoji, lamarin da ya haddasa mutuwar mutane a kalla 13, gami da raunana wasu fiye da 200.
A daidai wannan rana kuma, Ali Abdullah Saleh, shugaban kasar, ya bayyana wa manema labaru cewa, zai je kasar Amurka don samun jinya tare da ba da dama ga gwamnatin hadaka da aka kafa kwanan nan, ta samu sararin kimtsawa sosai domin babban zaben da aka shirya gudanarwa a badi. Shugaban ya ce zai samu jinya a kasar Amurka, sa'an nan zai dawo Yemen bayan da ya samu sauki. Sai dai kuma, ya yi tir da zanga-zangar da masu adawa da gwamnatinsa suke jagorantar.
A daren jiya 24 ga wata, an ba da labarin cewa, jama'a fiye da dubu 10 na ci gaba da yin zanga-zangarsu a cibiyar birnin Sana'a, inda suka yi kiran a gurfanar da shugaba Saleh a gaban kotu.(Bello Wang)