Mohammed Qahtan shi ne mai magana da yawun masu adawa da gwamnatin ya shaidawa kamfanin dillacin labarai na Xinhua cewa a matsayinsu na wakilai sun gana da wakilan shugaban kasar Abdul Saleh ciki har da mataimakinsa Hadi sa'an nan da manzon MDD wanda ya kawo ziyara kuma shine ke jagorantar tattaunawar amma duk da haka ba a samu ci gaba ba ko batun al'kawari,domin shugaba Saleh yana kan batunsa na kin mika ragamar mulkin kasar lami lafiya.
A nasa bangaren wani jami'in ofishin shugaban kasar kuma ya nemi a sakaye sunansa ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, yana ganin ba za a iya cimma wata yarjejeniya ba a tsakaninsu tun da bangaren masu adawa sun ki sassautawa.
Ya kara da cewa,kwamitin sulhu na MDD ya dage ganawar da zai yi da bangarorin kan matsayar kwamtin zartaswa na 2014 na kawo karshen rikicin na Yemen da aka shafe sama da watanni ana yin sa.
A ranar 10 ga wata ne manzon MDD Bin Omar, ya isa kasar Yemen dan isar da sakon kwamittin zartaswa na bukatar shugaba Saleh ya bada hadin kai ga yarjejeniyar kungiyar kasashen larabawa dake yankin tekun Gulf na mika mulkin kasar cikin lumana ga mataimakinsa Hadi dan kare kan shi daga shari'a.
Karo uku dai shugaba Saleh ya kauracewa sa hannu kan yarjejeniyar da kungiyar GCC ta gabatar a watan Aprilu. Kawo yanzu watanni goma kenan aka shafe ana zanga zanga a kasar.(SALAMATU).