in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin na fatan bangarori daban daban na kasar Yemen za su aiwatar da abubuwan dake shawarwari na GCC yadda ya kamata
2011-11-24 16:36:25 cri
Kakakin ma'aikatar harkokin waje na kasar Sin Liu Weimin ya yi bayani a yayin taron manema labaru da aka shirya a ranar 24 ga wata a nan birnin Beijing, inda ya maraba da sa hannun bangarori daban daban na kasar Yemen kan shawarwari na kwamitin hadin gwiwa na kasashen Larabawa na Gulf wato GCC da kuma shirin da suka tsara don aiwatar da shawarwarin. Liu ya ce, wannan muhimmin mataki ne da kasar Yemen ta dauka kan yunkurin tafiyar da mulkin wucin gadi na kasar, kasar Sin na fatan bangarori daban daban da abin ya shafa za su aiwatar da shawarwarin yadda ya kamata, domin sake maido da tsarin al'umma, da kuma tabbatar da zaman karko da samun bunkasuwar kasar. (Bilkisu)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China