in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta yi maraba da yadda aka kafa gwamnatin hadaka a Yemen
2011-12-08 16:45:20 cri

Hong Lei, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin, ya furta a ranar 8 ga wata a nan birnin Beijing cewa, kasar Sin ta yi maraba da yadda aka kafa wata gwamnatin hadaka a kasar Yemen.

A wajen taron manema labaru, Hong Lei ya amsa wata tambayar dangane da kafuwar gwamnatin hadaka a Yemen a ranar 7 ga wata, inda ya fadi cewa, kasar Sin na fatan ganin bangarorin kasar Yemen za su ci gaba da kokarin aiwatar da shawarwarin da kungiyar kasashen dake kewayen mashigin tekun Pasha (GCC) ta gabatar, sa'an nan su yi kokarin kau da sabani ta hanyar lumana, don farfado da tsari da oda a kasar cikin sauri, tare da tabbatar da kwanciyar hankali da samun ci gaban kasa. (Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China