Mista Xi ya bayyana hakan a cikin wata wasika da ya aike wa wasu malaman sa kai goma sha biyar da suka samu digirin jami'ar Baoding dake Hebei a shekarar 2000 kuma suke aiki tun lokacin a cikin wata makaranar sakandare dake yankin kabilar Uigur na jihar Xinjiang mai cikin gashin kanta dake arewa maso yammacin kasar Sin.
Kuna koyarwa a makarantun sakandare dake yankunan iyakokin yammacin kasa tun fiye da shekaru da dama kuma wannan sha'awa taku tana sosa rai matuka in ji mista Xi Jinping.
Haka kuma shugaban kasar Sin ya nuna yabo ga mutanen da suka dauki niyyar sa kai wajen taimaka wa bada ilimi a yankunan yammacin kasar Sin domin kishinsu ga cigaban tattalin arzki da na jama'a, har ma da hadin kan kabilun kasar.
Bautawa al'ummar kasa da kuma bada taimako wajen gina kasa hanya ce mai kyau da matasa ya kamata su bi, in ji shugaba Xi tare da nuna fatansa wajen ganin matasan kasar Sin rika yin aiki daga tushe domin cimma muradunsu. (Maman Ada)