in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Al'ummar Wukari dake jihar Tarabar Najeriya sun koka da dokar hana fita
2014-04-20 18:41:09 cri

Al'ummar garin Wukari na jihar Taraba dake tarayyar Najeriya sun koka da matsanancin halin da suka shiga na rashin wadatar abinci da ruwan sha, saboda dokar da aka kafa ta hana fita waje baki daya a garin, bayan wani mummunan tashin hankalin da ya yi sanadiyyar kashe mutane da dama tare da hasarar dukiya mai yawa.

Wani jami'in kungiyar ba da agaji ta Red Cross dake taimakawa mutanen garin na Wukari, Mr. Lucky Abio, ya ce mutane suna cikin matukar bukatar abinci da ruwa da kuma magunguna, saboda ba su da sukunin fita waje domin sayen wadannan abubuwa.

Ya ce saboda babu kowa a waje, wasu bata-gari suna fasa kantunan mutane suna musu sata, don haka yana da kyau a kyale mutane su samu zarafin fita ko da na gajeren lokaci ne domin su samo abinci da kayan bukatu.

Shi kansa mukaddashin gwamnan Jihar Taraba, Alhaji Garba Umar, ya bayyana cewa bai ji dadin abin da ya gani ba, a lokacin da shi da manyan jami'an gwamnatinsa da na tsaro suka ziyarci garin na Wukari.

Mukaddashin gwamnan ya jajantawa mazauna garin Wukari bisa abin da ya faru, yana mai cewa gwamnati za ta kara kaimin samarwa matasa aikin yi domin rage irin wannan rikicin.

Aku Uka na Wukari, kuma shugaban majalisar sarakunan jihar Taraba, Dr. Shekarau Angyu, ya bayyana takaicin wannan rikici na Wukari, sa'annan ya roki gwamnati da ta sassauto da dokar hana fita da aka kafa. (Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China