in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An bude wani gidan asibiti a garin Bimbo na kasar Afrika ta Tsakiya da kasar Sin ta bada taimako wajen gina shi
2011-10-05 19:49:14 cri

A ranar Talata da ta gabata, shugaban kasar Afrika ta Tsakiya, Francois Bozize da jakadan kasar Sin dake kasar Mista Sun Haichao sun jagaranci wani bikin bude wani asibiti wanda zai iya daukar gado 100 da kasar Sin ta bada taimako wajen gina shi a Bimbo babban garin da kegundumar Ombella M'Poko a kudancin birnin Bangui.

Asibitin Bimbo da aka gina bisa kimanin muraba'in mita 5000, na kunshe da dakin na'urorin aikin likita, dakin jinya da wasu dakunan karbar marasa lafiya daban daban har guda uku, dakin kula da ciwon dake da nasaba da fatar jiki, dakin binciken lafiyar mata, dakin harhada magani, dakin zaunar da masu ciwo, dakin kula da masu ciwon ido, dakin na'urar binciken jiki, sashen kula da ciwon hakora da kuma dakin yin tiyata.

Ministan kiwon lafiyar kasar, Jean Michel Mandaba ya nuna cewa asibitin Bimbo shi ne a matsayin na farko da zai taimakawa wannan yanki ta fuskar kiwon lafiya wanda ya hada da gundumomin Ombella M'Poko da Lobaye, sa'an nan kuma zai taimaka wajen rage cunkoson da ake fuskanta a asibitocin dake birnin Bangui.

Gwamnatin kasar Sin ta yi alkawarin bada kayayyakin aikin likita da darajarsu ta kai RMB miliyan 10 kwatankwacin dalar Amurka miliyan 1.5 domin ganin cewa wannan asibiti ya fara aiki yadda ya kamata in ji jakadan kasar Sin dake kasar.

Kasashen Sin da Afrika ta Tsakiya sun rattaba hannu kan wasu jarjejeniyoyi 30 da suka shafi dangantakar tattalin arziki data fasaha. Haka kuma yanzu haka akwai wasu tsare tsaren ayyukan cigaba kusan 50 da ke tafe, wanda aka kulla tsakanin kasashen biyu wadanda aka kimanta darajarsu zuwa RMB miliyan 320 kwatankwacin dalar Amurka miliyan 50 a cewar wani jami'in ofishin jakadancin kasar Sin.(Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China