Gwajin dai wanda aka gudanar a ranar 26 ga wata nan, ya samu halartar dalibai dubu biyar.
Tun da fari hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA ta nemi a kammala aikin ginin filayen wasan kasar ta Brazil ne kafin ranar 31 ga watan Disambar bara, amma uku daga wadannan filayen basu kai ga kammala ba a kan lokaci. Inda filin wasan na St Paul Corinthians ya kasance daya daga cikin wadannan filaye uku. An ce, ana kokarin gudanar da aikin ginawa tare da kafa kujerun wucin gadi dubu 20, domin biyan bukatun 'yan kallo yayin gasar cin kofin na duniya.
Za a buga wasan farko na wannan gasa ne dai a ran 12 ga watan Yuni tsakanin kungiyar Brazil da Croatia.
Babban jami'in kwamitin gudanarwar hukumar FIFA Ricardo Strahd ya bayyana cewa, za a kaddamar da filin wasan na St Paul Corinthians a ran 18 ga watan Mayu. Kuma a ran 26 ga wannan watan da muke ciki, dilibai dubu 5 sun yi aikin gwaji a cikin sa. Wadannan dalibai sun zauna a wani wuri cikin filin, inda suka rera wakar kungiyar Corinthians, yayin da kuma aka gayyaci wasu daga cikin su cikin filin, suka yi bugun daga kai sai mai tsaron gida. (Amina)