in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Tsohon kocin Barca Tito Vilanova ya rasu
2014-05-01 17:20:13 cri
Tsohon kocin kungiyar Barcelona ta Sifaniya Tito Vilanova ya rasu a ranar juma'a 25 ga wata, bayan ya sha fama da cutar sankara, wadda aka gano yana dauke da ita a shekarar 2011.

Haifaffen kasar Sifaniya, Tito ya rasu yana da shekaru 45 a duniya. Kamar dai yadda bayanin hakan ke kunshe cikin wani jawabi da aka sanya a shafin yanar gizon kulaf din na Barcelona.

An ce an yiwa Tito aiki a ranar Alhamis, kafin daga bisani yanayin da yake ciki ya kara tsananta.

Tito wanda shi ne kocin kungiyar Barcelona na 50, ya kasance mataimaki ga babban kocin kungiyar Pep Guardiola har tsahon kakar wasanni hudu, kafin daga bisani ya gaje shi a shekarar 2012.

Ya kuma jagoranci kungiyar a kakar wasanni ta 2012 zuwa 2013, amma bai sami damar halartar wasannin watanni uku na karshen kakar ba, sakamakon yanayin lafiyar sa da ya kara tsananta a lokaci. Daga bisani kuma a watan Yulin bara, ya bayyana yin murabus daga aikinsa, aka kuma maye gurbin sa da Gerardo 'Tata' Martino.

Kulaf din Barcelona dai ya bayyana matukar alhinin sa ga rasuwar tsohon kocin na sa, tare da mika ta'aziyyar rasuwar sa ga iyalai, da 'yan uwa, da ma daukacin masu goyon bayan kulaf din, da masoyan kwallon kafa baki daya.

An kuma bayyan cewa Barcelona za ta bude wata rajistar musamman a filin wasan ta na Camp Nou, domin masu burin rubuta sakon ta'aziyar su.

Cikin manyan kusoshin kulaf din da suka bayyana alhinin rasuwar Tito hadda shugaban kulaf din Josep Bartomeu, wanda a sakon sa na yanar gizo, ya ce "Barcelona na godewa gudummawar da ka bayar ta mutuntaka da ta fannin wasanni. Godiya gare ka game da dukkanin abinda ka koyar da mu. Allah ya ji kan rai."

Shi ma wani tsohon dan wasan Barcelona Lobo Carrasco cewa yayi "ina cikin bakin ciki da bacin rai. Tito bai karaya ba, amma mutuwa ta dauke shi daga gare mu. Tito misali ne na mutumin da ya san mece ce gasa."

Bugu da kari shi ma kocin Chelsea Jose Mourinho, wanda ya taba tsokanewa Tito ido yayin da yake horas da kulaf din Real Madrid, a wasan su na karshe na Supercup, a shekarar 2011 cewa yayi "Rana ce ta bakin ciki, ina bayyana matukar jimami na".

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China