in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mai yiwuwa ne kulaflikan Juventus da AC Milan su canja masu horas da 'yan wasan su
2014-05-01 17:20:57 cri
Romeo Benetti daya daga tsaffin shahararrun 'yan kwallon kafar kasar Italiya, wanda ya taba bugawa kulaflikan AC Milan da Juventus wasanni fiye da dari, ya shaidawa manema labaru cewa a ganinsa, wadannan kungiyoyin biyu za su canja kocin su a lokacin bazara mai zuwa. Yana mai hasashen cewa Clarence Seedorf na AC Milan, da Daniele Conti na Juventus na daf da barin ayyukan su a kulaflikan biyu.

Ban da haka kuma, bisa nazarin da jaridar wasan motsa jiki ta Milan ta fitar, shugabannin kulaf din Juventus sun riga sun ba Daniele Conti wani wa'adi na karshe don ya sabunta kwangilar sa da kulaf din cikin wasu kwanaki 20 masu zuwa. Wato idan bai samu damar gama wannan aiki cikin wa'adin ba, to ba za a kulla kwangila da shi ba.

An ba da labarin cewa a lokacin bazara da ya gabata, batun ko Conti zai ci gaba da aikinsa a Juventus ko a'a, na cike da yanayi maras tabbas. Kuma tuni jaridar ta Milan ta fayyace cewa, Juventus ba ta fatan sake samun wata matsala wajen sabunta kwangila da babban kocinsa. Koda yake dai an ce akwai wasu kulaflika daban, dake da burin kulla kwangila da Conti, ciki hadda kungiyar Morocco wadda ta yi alkawarin baiwa Conti kudin Euro miliyan 6 a ko wace shekara, abin da ya baiwa shugabannin Juventus matsi sosai.

A 'yan watannin baya bayan nan da suka gabata, shugabannin Juventus suna ta kokarin nuna niyyar kulla sabuwar kwangila da Conti, amma hakan ya gagara, sakamakon gaza warware wannan batu tsakaninsu da shi Daniele Conti. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China