Bisa ga sakamakon wala-walar dai kasar Burma, da Iran, da Thailand da kuma Yemen na rukuni ne na daya wato rukunin A. Sai kuma Uzbekistan, da Australia, da hadaddiyar daular Larabawa, da Indonesia dake rukunin B. Akwai kuma kasar Koriya ta Kudu, da Japan, da Sin da kuma Vietnam a rukunin C. Yayin da kuma Iraqi, da Koriya ta Arewa, da Qatar da kasar Oman ke rukuni na hudu wato rukunin D.
Za dai a buga wannan gasa ne a biranen Nay Pyi Taw da Yangon na kasar Burma daga 9 zuwa 23 ga watan Oktobar dake tafe.