Bisa kuma tsari, hukumar ta UEFA za ta nazarci, tare da tantance bukatar da birane masu fatan daukar bakuncin wasannin suka gabatar, kafin daga bisani ta mika rahotonta ga babban kwamitin zartaswar ta. Kaza lika ana sa ran bayyana birane 13 da za a amince su karbi bakuncin gasar a ranar 19 ga watan Satumbar shekarar nan, a birnin Geneva na kasar Switzeland.
A yayin wani taron kwamitin zartaswar hukumar ta UEFA na shekarar 2013 ne dai aka yanke shawarar baiwa birane 13 da za a zaba, damar daukar bakuncin zagayen karshe, na gasar cin kofin kasashen na Turai na shekarar ta 2020.