Kafin haka, an dakatar da aikin ginin babban filin wasa na Itaquerao dake birnin Sao Paulo a ranar 31 ga watan Maris, bayan da aka samu mutuwar wani ma'aikaci na 3 cikin watanni 4 da suka gabata a filin.
Yayin da take fuskantar zargin da aka yi mata cewa ta yi sakaci da aikinta, ma'aikatar kwadagon ta fidda wata sanarwa a ranar 3 ga watan Afrilun nan, inda ta ce tana kokarin sa ido kan aikin da ake gudanarwa na gyaran fuskar filin wasan Itaguerao, don tabbatar da samun biyan bukata, a fannonin kiwon lafiya da tsaro. Ta ce an gudanar da bincike karo 9 kan ayyukan ginin filin wasan na Itaquerao, hakan ne ma ya sa aka gano karya dokokin da aka yi a yayin aikin, aka kuma dakatar da aikin nan take.
Sai dai a nasa bangaren, shugaban 'yan kwadago reshen yankin Sao Paulo, mista Luiz Medeiros, ya bayyanawa wakilin jaridar Folha de S.Paulo cewa, ya dauke kai daga matsololin da ake fuskanta a aikin gyaran fuskan filin wasan. A cewarsa, in ban da filin wasan na cikin filayen da za a gudanar da gasar cin kofin duniya a cikin sa, da tuni an dakatar da aikin.
Sai dai ganin yadda kalaman nasa suka fusata gwamnatin kasar, Medeiros ya ce waccan magana da ya yi, ra'ayi ne kawai na kashin kansa.
A wannan fili ne dai na Itaquerao, aka shirya gudanar da wasanni 6 na cin kofin duniyar dake tafe, ciki har da wasan farko tsakanin Brazil da Croatia a ranar 12 ga watan Yuni.(Bello Wang)