in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Babban kocin kungiyar Ghana Appiah na kokarin share fage domin gasar cin kofin duniya
2014-04-16 17:46:32 cri

Kwesi Appiah, wanda ya taba zama kyaftin din kungiyar wasan kwallon kafan kasar Ghana, kuma kocin kasar na gida na farko cikin shekaru 10. A matsayinsa na wanda zai jagoranci kungiyar zuwa gasar cin kofin duniya na wannan karo, ana sa ran ganin Appiah ya kai kulaf din na Ghana gaba, bisa zagayen da ta tsaya a karon da ya wuce na wasan dab da kusa da na karshe.

Nada Appiah matsayin babban kocin Ghana, ya nuna wani sauyin yanayi kan manufar hukumar wasan kwallon kafar Ghana, wadda a shekarun baya ta rika baiwa wasu Turawa wannan aiki, musamman ma 'yan Serbia. Har wa yau hakan ya dace da sabon yanayin da aka fara gani a nahiyar Afirka, inda aka fara karkata ga masu horar da 'yan wasa 'yan asalin kasashen Afirka, domin aikin horas da 'yan wasan nahiyar.

Baya ga Appiah, Stephen Keshi, babban kocin kungiyar Najeriya, shi ma ya jagoranci kungiyar kasar sa, wajen lashe kofin nahiyar Afirka a bara.

A nasa bangare Appiah ya taba bayyanawa 'yan jarida cewa, dalilin da ya sa yake ganin zai iya cimma nasara shi ne, kasancewar sa cikin kalilan a masu horar da 'yan wasan kungiyoyin kasashe daban daban 'yan asalin Afirka, mai kwarin zuciya, wanda ba zai yarda a juya shi ba.

Appiah ya dade yana aiki a matsayin mataimakin kocin kungiyar Ghana, kuma ya taba jagorantar kungiyar 'yan kasa da shekaru 23 wajen samun lambar zinare a gasar cin kofin nahiyar Afirka da ya gudana a shekarar 2011.

Amma a matsayin babban kocin kungiyar Ghana, wannan ne karon farko da zai halarci babbar gasar kasa da kasa. Baya ga gasar cin kofin Afirka ta shekarar 2013, inda Burkina Faso ta lashe Ghana a wasa na kusa da na karshe ta hanyar bugan daga kai sai mai tsaron gida, abin da ya ba mutane mamaki. Ko da yake rashin samun nasara a waccan karo bai yi wata barazana ga aikin Appiah, sai dai hakan shi ma ya nuna cewa jami'an hukumar kwallon kafan kasar Ghana na jiran ganin Appiah ya nuna kwarewarsa a gasar cin kofin duniya da za a gudanar a Brazil.

A wani abu mai kama da mayar da martani, kungiyar Ghanan ta nuna karfinta a wasannin share fagen gasar cin kofin duniya, inda ta lashe Masar, wadda ta taba zama zakarar nahiyar Afirka karo 7, da ci 6 da 1. Wasannin dake jiran Appiah a zagayen rukuni farko na gasar cin kofin duniya da suka hada da karawa da Jamus, da Portugal, da Amurka, za su kasance babbar jarrabawa gare shi, wadda kuma sakamakonta zai tabbatar ko zai iya kiyaye mukaminsa na babban kocin kungiyar ta Ghana ko kuwa a'a. (Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China