Dan wasan ya ji rauni ne lokacin da ya buga wata kwallo da karfi, a yunkurin farke kwallon da Raheem Sterling ya ciwa Liverpool, kafin a tafi hutun rabin lokaci.
Daga bisani, an maye gurbin Toure da Javi Garcia, amma kulob din Manchester City ya kara fadawa wani yanayi mai wuya, bayan da dan wasan bayan Liverpool Martin Skrtel ya ci ma kungiyarsa kwallo ta 2.
Bayan hutun rabin lokaci, City ta yi kokarin farke kwallon da Liverpool ta zura mata, bisa kwallon da David Silva ya ci, da wadda Glen Johnson ya ci gidansu. Amma Philippe Coutinho ya sake ciwa Liverpool kwallo ta uku, mintuna 12 kafin tashi wasan, wanda hakan ya tabbatarwa Liverpool nasarar a karshen wasan.
Yayin da yake magana da manema labaru bayan wasan, shugaban kulob din Manchester Manuel Pellegrini, ya ce da wuya Yaya Toure ya ci gaba da taka leda a wasannin da suka rage a kakar wasan da ake ciki.
A daya bangaren kuma, karatowar gasar cin kofin duniya da ke tafe a watan Yuni mai zuwa, ta sanya shakku kan ko Yaya Toure zai iya farfadowa cikin lokaci, har ya buga ma kasarsa ta Cote d'Ioire wasa a wannan babban gasa ta duniya. (Bello Wang)