A wannan karo, kungiyar na tare da 'yan wasa masu kwarewa, da ake sa ran ganin za su taimaka ma ta samun gagarumar nasara a gasar ta bana.
'Yan wasan kungiyar da suka hada da Kompany, Hazard, da Courtois, kakar wasanni ta bana sun taka rawar gani a kuloflikan da suke wa kwallo, a Ingila da Sifaniya, karkashin inuwar tsarin manyan gasannin duniya irin na Premier League da La Liga. Hakan ya sa kyaftin din kungiyar Belgium Vincent Kompany, ya fara tunanin yiwuwar lashe kofin duniya, yayin wata tattaunawa da yayi da 'yan jarida.
Duk da cewa Belgium ba ta sake samun damar zama zakara a wata babbar gasar kasa da kasa ba a baya bayan nan, tun bayan lashe kofin gasar Olympics a shekarar 1920 da ta yi. Sai dai a wannan karo ta tara 'yan wasa fitattu, za kuma ta kara a rukuni na 8 wato na H tare da Rasha, da Koriya ta Kudu, da Aljeriya, kuma duba da tasirin da za ta iya yi a wannan rukuni, ake sa ran ganin ta samu damar fitowa daga rukunin don shiga wasannin zagaye na biyu.
Ban da haka kuma, wasu kwararrun 'yan wasan da kungiyar ke da su, na iya ciyar da ita gaba a wannan gasa ta cin kofin duniya dake tafe. Ga misali Thibaut Courtois da kulof din Chelsea ya ba da aronsa ga Atletico Madrid, ya riga ya zama mai tsaron gida mafi kwarewa a gasar La Liga. A kakar wasanni da ta gabata, Courtois ya taka muhimmiyar rawa wajen taimakawa Atletico Madrid lashe kulob din Real Madrid, a karawarsu ta cin kofin Copa del Rey na kasar Sifaniya.
A nasa bangaren, dan wasan gaba Eden Hazard shi ma yana kara nuna kwarewarsa, a kokarin ciyar da kulob dinsa na Chelsea gaba, a gasar Premier ta bana. Hakan ya sanya matsayinsa daukaka a idanun manajan kulof din Jose Mourinho.
A gasar cin kofin duniya da ta gabata, an cire Belgium ne a zagayen kungiyoyi 16, bayan da zakarar gasar a wancan karo wato Brazil ta lashe ta. Sai dai a wannan karo, Marc Wilmots, babban kocin kungiyar Belgium din na kokarin ganin kungiyar ta taka rawar gani sama da matsayin ta na baya. (Bello Wang)