in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ancelotti yayi mamakin gazawar Barcelona
2014-04-16 17:50:26 cri
Kocin Real Madrid Carlo Ancelotti ya ce a gaskiya ya yi mamakin jin cewa Barcelona ta sha kashi a hannun Granada da ci daya mai ban haushi, yayin wasan da ta buga a ranar Asabar, a daidai gabar da Real Madrid ta lallasa Almeria da ci 4 da nema.

Wannan ne dai karo na biyu da Baca ta rasa nasarar wasannin ta cikin mako guda, baya ga fitar da ita da aka yi daga gasar cin kofin zakarun turai a wasan kusa da na kusa dana karshe. A hannu guda kuma Real Madrid na ci gaba da matsa kaimin nuna tasirin ta a gasar ta Laliga, dama shirin ta na fuskantar wasan kusa da na karshe, a gasar cin kofin zakarun turai.

Za dai a buga zagayen farko na wasannin kusa da na karshen ne a gasar cin kofin zakarun turai ne a ranekun 22 da 23 ga watan Afirilun nan, sai kuma zagaye na biyu a ranekun 29 da 30 ga watan na Afirilu. Inda Real Madrid za ta kara da mai rike da kambin gasar wato Bayern Munich, yayin da kuma kulaf din Chelsea na Ingila zai fafata da Atlentico Madrid shima na Sifaniya.

Don gane da wancan wasa da Granada ta lashe Berca kuwa, cokin Madrid ya kara da cewa, yayi imanin za a ci gaba da dauki ba dadi har ya zuwa karshen gasar, kuma daukacin kulaflikan dake buga gasar ta Laliga zasu yi iyakacin kokarin su wajen kai bantan su.

Bisa jadawalin gasar Laliga ta bana dai, yanzu haka Atletico Madrid ce ke kan gaba da maki 82, sai Real Madrid dake biye da maki 79, yayin da kuma Barcelona ke matsayi na uku da maki 78. A can kasa kuwa Getafe ce ke matsayi na 18 da maki 31, sai Almeria da ke na 19 da maki 30, sannan akwai Real Betis a matsayi na 20 da maki 22.(Saminu Alhassan Usman)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China