in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
AC Milan na ci gaba da kare kambin ta
2014-04-16 17:48:03 cri
Kulaf din AC Milan na ci gaba da kare kambin sa, a gasar Serie A ta kasar Italiya, bayan da a ranar Lahadin da ta gabata ya lashe wasan da ya buga a gida, da takwaransa na Catania da ci daya da nema. Nasarar da ta bashi damar lashe wasanni hudu ke nan a jere.

Dan wasan Milan Riccardo Montolivo, wanda yayin wasan kulaf din na Milan da Catania na baya, ya ciwa kulaf din nasa kwallaye 3, a wannan karo ma shi ne ya jefa kwallo daya tak da aka ci a wasan na Lahadi cikin minti na 23 da take wasa.

Kafin dai kammalar wasan AC ta matsa kaimin kara yawan kwallayen ta sai dai hakar ta bata tadda ruwa ba. Koda yake AC Milan da a baya ta taba daukar kofin gasar ta Serie A har sau 18, ba ta nuna wata bajimta ta daban ba a wannan kaka, a hannu guda masu fashin baki na ganin nasarar da take samu yanzu haka za ta bata karin karfin gwiwar fuskantar kalubalen dake gabatan ta, musamman a yanzu da take rage tazarar dake tsakanin ta da Inter Milan.

Ga kocin AC Milan Clarence Seedorf, babban abin lura shi ne wasannin kulaf din na gaba, ba wai matsayin su a teburin gasar ba.

"A koda yaushe na kan ce bana ko kallon teburin gasar, domin na san halin da ake ciki, muna da sauran wasanni, kuma dole ne mu maida hankali, mu kuma jira ganin yadda za ta kaya a karshen kaka" A kalaman cokin AC Milan Seedorf.

Yanzu dai haka AC Milan na kasan Inter Milan da maki 5 a teburin gasar ta Serie A, a matsayi na 8 da maki 48. A saman jadawalin kuwa, kulaf din Juventus ne ke matsayin farko da maki 87. Sai Roma a matsayi na biyu da maki 79, yayin da kuma Napoli ke matsayi na uku da maki 67.(Saminu Alhassan Usman)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China