in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Dortmund ta girgiza Bayern a teburin gasar Bundesliga
2014-04-16 17:49:12 cri
Kulaf din Borussia Dortmund ya girgiza Bayern Munich da ci 3 da nema, a wasan mako na 30 da suka buga ranar Lahadi. Matakin da ya haifarwa Munich din rashin nasara ta biyu a jere cikin wasannin baya bayan nan da ta buga. Duk dai da hakan Bayern Munich ta ci gaba da rike matsayin ta na daya a teburin gasar Bundesliga ta kasar Jamus da maki 78, inda ta baiwa Dortmund dake matsayi na biyu tazarar maki 17. Yayin da ita kuma a nata bangare Dortmund ke ci gaba da tabbatar da tasirin ta a wannan gasa, da ma tabbashin halartar gasar ta badi.

A wasan ranar Asabar kuwa Hamburg ta tashi daya da biyu da Hannover, yayin da Stuttgart ta yi kunnen doki da Borussia Monchengladbach 1 da 1. Kulaflikan biyu dai na kokarin kaucewa fadawa "relegation".

Baya ga Bayern Munich da Dortmund dake matsayi na daya da na biyu a jadawalin gasar ta Bundesliga, akwai kuma kulaf din Schalke dake matsayi na uku da maki 58, yayin da kuma Bayer Liverkusen ke matsayi na 4 da maki 51.

Can kasan teburin kuwa Hamburg ce ke matsayi na 16 da jimillar maki 27, sai Nurnberg dake na 17 da maki 26. Yayin da TSV ke karshe da maki 25.

Cikin kuma kulaflikan da wasan wannan mako ya yi wa dadi akwai Wolfsburg wadda ta matsa sama, bayan ta lallasa Nuremberg da 4 da 1. Sai kuma Mainz, wanda ya doke Bremen da ci 3 da nema.(Saminu Alhassan Usman)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China