Ban, wanda ya bayyana hakan a jawabin sa na bude taron kwamitin sulhun majalissar a ranar Jumma'a 14 ga wata, ya kara da kashedin cewa, akwai alamun dada tabarbarewar al'amura a kasar.
Daga nan sai ya bukaci daukacin sassan masu ruwa da tsaki, da su dukufa, wajen ganin an tallafawa al'ummar wannan kasa da yaki ya daidaita.
A wani ci gaban kuma Mr. Ban ya jinjinawa kokarin kungiyoyin ECCAS, da AU, bisa himmar su ga cin nasarar shirin warware matsalar Afirka ta tsakiyar, da ma gudummawar da suka bayar wajen kafuwar rundunar wanzar da zaman lafiya ta MISCA. Har ila yau baban sakataren MDDr ya yabawa gwamnatin kasar Faransa, bisa gudummawar soji da ta bayar, tare da fatan kungiyar hadin kan turai ta EU, ita ma za ta bada tata gudummawa.
Kawo yanzu dai dubban mutane ne suka rasa rayukan su a jamhuriyar Afirka ta tsakiyar, sakamakon kisan gillar da magoya bayan kungiyar Seleka ta Musulmi, da Anti-Balaka ta mabiya addinin kirista ke yiwa fararen hula. (Saminu Alhassan Usman)