in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Park Geun-hye ta yi rantsuwar kama aikin a matsayin shugabar Koriya ta Kudu
2013-02-25 16:19:29 cri

A ranar 25 ga wata da safe ne, aka yi bikin rantsuwar kama aikin zababbiyar shugabar Koriya ta Kudu Park Geun-hye, a dandalin majalisar dokokin kasar. A cikin jawabin da ta yi a yayin bikin, Park Geun-hye ta gabatar da ra'ayin farfado da tattalin arzikin kasar, da kawo alheri ga jama'a, da kuma raya al'adun kasar.

Haka kuma, a cikin jawabin nata, Park Geun-hye ta ce, bisa ra'ayin da ta gabatar, za ta shugabanci jama'a don sake kago abin al'ajabi a kasar. A sa'i daya kuma, ta yi kira ga Koriya ta Arewa da ta dakatar da shirinta na raya nukiliya ba tare da bata lokaci ba, ta kuma girmama yarjejeniyar da aka daddale a baya, don sake kama hanyar yin shawarwari cikin lumana.

Park Geun-hye ta zama mace ta farko a cikin tarihin jerin shugabannin kasar ta Koriya ta Kudu.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China