in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mutane 9 sun rasu sakamakon nutsewar jirgin ruwan fasinjan Koriya ta Kudu
2014-04-17 10:58:12 cri
Wani jirgin ruwan fasinjan kasar Koriya ta Kudu mai dauke da fasinjoji 475 ya nutse da sanyin safiyar ranar Laraba, a wani wuri dake kudu maso yammacin kasar. Lamarin da ya haddasa mutuwar mutane 8, da bacewar mutum 287, yayin da kuma aka ceto mutane 179.

'Yan sandan kasar sun bayyana cewa, canja hanyar da jirgin ruwan ya yi cikin gaggawa ce ta haddasa motsawar kayayyakin dake cikinsa, wanda kuma hakan ya sanya shi kifewa ya kuma nutse nan take.

A safiyar Alhamis din nan kuma 'yan sandan ruwan yankin sun ci gaba da aikin ceton da suke yi, duk da yanayin gudun ruwan, da kuma karancin haske a karkashinsa dake yiwa aiki tarnaki. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China