in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Firaministan kasar Sin zai yi ziyara a wasu kasashe hudu dake nahiyar Afirka
2014-05-01 01:00:25 cri

Nan da 'yan kwanaki kadan masu zuwa ne ake sa ran firaministan kasar Sin Li Keqiang, zai tashi zuwa kasashe hudu dake nahiyar Afirka domin gudanar da ziyarar aiki.

A jiya Laraba 30 ga watan Afrilu ne ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ta kira wani taron manema labaru kan wannan batu, inda mataimakin shugaban ma'aikatarministan harkokin wajen Sin Zhang Ming ya bayyana cewa, wannan ne karo na farko da firaministan sabuwar gwamnatin Sin zai kai ziyara a nahiyar Afirka. Matakin da ke da muhimmanci kwarai wajen kara sada zumunta, da zurfafa sabuwar dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare tsakanin Sin da kasashen na Afirka.

Game da wannan ziyara abokiyar aikinmu Fatima ta hada mana wannan rahoto.

A ranar 4 ga watan Mayun nan ne firaministan kasar Sin Li Keqiang zai tashi zuwa nahiyar Afirka. Yayin ziyarar ta kwanaki 7, Mr. Li zai kai ziyara kasashen Habasha, da Nijeriya, da Angola, da kuma Kenya. Game da yadda aka zabi wadannan kasashe hudu da firaministan na Sin zai ziyar ta a wannan karo, Mista Zhang ya bayyana cewa,

"A wannan karo, firaminista Li zai kai ziyara a gabas da yamma da kuma kudancin Afirka ne. Ana iya cewa, ziyarar ta sa za ta kasance wani muhimmin aikin diplomasiyya a da ya shafi duk fadin nahiyar Afirka. Hedkwatar kungiyar tarayyar kasashen Afirka ta na Habasha, kuma an dauki birnin Addis Ababa a matsayin hedkwatar siyasa da diplomasiyya ta nahiyar Afirka. Bayan haka, Nijeriya c e ke kan gaba wajen yawan al'umma a nahiyar, kuma ita ce mafi karfin tattalin arziki a nahiyar. Dadin dadawa, Angola na daya daga cikin kasashen Afirka da suka fi samun ci gaba cikin sauri a cikin 'yan shekarun baya bayan nan, kuma kasashen dake da karfi sosai wajen samun bunkasuwa. Kenya kuwa, ba kawai ta kasance mai muhimmanci a Afirka ba ne kadai, har ma da kasancewar ta kasa daya tak dake da ofishin shirin lura da muhalli na MDD ko UNEP a takaice."

Har ila yau a ziyarar firaminista Li, za a iya ganin cewa, akwai wasu muhimman ayyuka da za su gudana, ban da shawarwari, da ganawa a fannin siyasa.

A kasar Habasha, kasa ta farko da zai ziyarta, firaminista Li zai halarci wani bikin kammala kafa wata babbar hanyar mota, da yin shawarwari da masu ruwa da tsaki a harkar cinikayyar Sin da na nahiyar Afirka da dai sauransu. A Angola kuma, firaminista Li zai yi shawarwari da kamfanonin Sin, da wakilan jama'ar Sin kan batun rayuwar jama'a a ketare.

Bisa labarin da aka bayar, an ce, a lokacin ziyarar, firaminista Li zai gabatar da muhimman jawabai guda biyu. A hedkwatar kungiyar AU, zai fitar da tsarin hadin gwiwa tsakanin Sin da kasashen Afirka a sabon zamani. Bisa goron gayyatar dandalin tattaunawar tattalin arzikin duniya kuma, firaminista Li zai halarci taron koli na Afirka, na dandalin tattaunawar tattalin arzikin duniya da za a kira a birnin Abuja, fadar gwamnatin Nijeriya, inda zai yi jawabi kan hanyar da za a bi don karfafa hadin gwiwa tsakanin Sin da kasashen Afirka, a kokarin cimma burin samun bunkasuwa tare, da kuma yin hadin gwiwa tsakanin Afirka da sauran kasashen duniya.

Ko mene ne ma'anar wannan ziyara ga bunkasar dangantaka tsakanin Sin da kasashen Afirka a nan gaba? Zhang Ming ya furta cewa,

"A ziyararsa, firaminista Li zai yi musayar ra'ayi da shugabannin kasashen Afirka, kan zurfafa hadin gwiwa tsakanin bangarorin biyu, da cimma burin samun bunkasuwa tare da dai sauransu. Kuma zai gabatar da manufofin da Sin ta dauka kan kasashen Afirka a cikin sabon zamani. Sin na fatan za a kara kuzari ga bunkasa dangantaka tsakaninta da kasashen Afirka karkashin wannan ziyara, ta yadda kasashen duniya za su kara mai da hankali ga zuba jari a Afirka, a kokarin samar da yanayi mafi kyau ga bunkasa nahiyar."

Karkashin dangantakar abokantaka tsakanin Sin da Afirka, hadin gwiwa a fannonin tattalin arziki da cinikayya na taka muhimmiyar rawa tsahon lokaci. Ko a wannan karo wane irin babban kuduri firaminista Li zai tafi da shi Afirka? Mataimakin ministan kasuwanci na Sin, Zhang Xiangchen ya bayyana cewa, 

"Za a samu babban sakamako a fannin tattalin arziki da cinikayya a wannan karo, ciki da akwai yarjeniyoyi tsakanin gwamnatocin kasashen, da aikin hadin gwiwa tsakanin hukumomin hada hadar kudi da kamfanoni, da suka kunshi fannoni da yawa, da hanyoyin hadin gwiwa iri iri. Matakin da zai bayyana hanyar da za a bi wajen bunkasa hadin gwiwa tsakanin Sin da kasashen Afirka a fannonin tattalin arziki da cinikayya a nan gaba."

Da yake karin haske don gane da hakan Mista Zhang Ming ya bayyana cewa, a wannan ziyara ta firaminista Li ta wannan karo, Sin da kasashen Afirka za su rattaba hannu kan yarjeniyoyi kimanin 60, wadanda za su shafi fannoni da dama, ciki hadda siyasa, da tattalin arziki, da cinikayya, da al'adu. Sauran fannonin su ne, na kiwon lafiya, da aikin noma, da horar da kwararru da dai sauransu.(Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China