in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Li Keqiang ya gana da mahalarta taron shekara-shekara na dandalin tattaunawa kan bunkasuwar kasar Sin
2014-03-25 14:41:28 cri

A ran 24 ga wata da yamma a nan birnin Beijing, firaministan kasar Sin Mista Li Keqiang, ya gana da wakilan kasashen ketare, da suka halarci taron shekara-shekara na 2014, na dandalin koli dangane da tattaunawa kan bunkasuwar kasar Sin.

Shugabannin manyan kamfanoni 500 na duniya, da kwararru daga shahararrun jami'o'in duniya, da hukumomin nazari, da darektocin Bankin Duniya, da kuma kungiyoyin hadin gwiwar tattalin arziki da yawansu ya zarta 70 ne suka samu halartar ganawar.

Li Keqiang ya ce, 'kasar Sin da ke zurfafa gyare-gyare daga dukkan fannoni' taken taro ne da ya dace da yanayin da ake ciki yanzu haka a kasar Sin.

Ya kara da cewa idan har kasar Sin tana fatan sauya hanyar da take bi wajen samun bunkasuwar tattalin arziki, daya daga manyan ayyukan dake gabanta shi ne inganta kirkire-kirkire. Ya ce kamata ya yi a kyautata tsari, a kuma kara amfani da manufofin da aka zartas yayin gwaje-gwaje, domin samar da moriya ga yankunan kirkire-kirkire a kasar. Baya ga batun neman kyakkyawan sakamako daga fasahohi, da kara habaka manufofin a sassan kimiya da fasahohi da hukumomin, don sa kaimi ga masu nazari wajen yin kirkire-kirkire.

A sa'i daya kuma ya kamata a mai da hankali kan aikin kare ikon mallakar ilmi, da inganta kafa dokoki da aiwatar da su, da kara karfin yanke hukuncin ga wadanda suka aikata laifuffuka, don kare moriyar kasa. Haka kuma Li ya yi fatan wasu kasashe za su soke shingen da suke yiwa kasar Sin ba bisa ka'ida ba, musamman game da batun cin gajiyar fasahohin zamani da suke fitarwa zuwa kasar Sin.

Wasu daga mahalarta ganawar sun bayyana cewa, bunkasuwar kasar Sin tana da muhimmanci matuka ga bunkasuwar tattalin arzikin duniya. Suna masu bayyana yabo ga gwamnatin kasar ta Sin, don gane da zurfafa gyare-gyaren da take yi. Suna masu imanin cewa, yanayin zuba jari a Sin zai kara samun kyautatuwa, matakin da zai kara samar da dama ga kamfanonin Sin da na kasashen waje. (Danladi)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China