in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Firaminista Sin ya tattauna da takwaransa na Australia kan aikin laluben jirgin saman Malaysia da ya bace
2014-04-30 21:22:59 cri
A yammacin yau Laraba 30 ga wata, firaministan kasar Sin Li Keqiang ya buga waya ga takwaransa na Australia Tony Abbot.

Li Keqiang ya bayyana cewa, yanzu aikin laluben jirgin saman Malaysia da ya bace ya shiga wani sabon mataki.inda Jiragen ruwa na Australia, da na Malaysia, da na Sin za su ci gaba da aikin laluben, tare da mayar da hankali kan neman jirgin a karkashin ruwa. Ko da yake za a gamu da matsaloli masu yawa cikin dogon lokaci, amma dole ne a ci gaba da wannan aiki akai-akai, wannan ne alhakin da ya kamata a dauka don faranta ran iyalan fasinjojin dake jirgin saman.(fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China