Babban darektan mai kula da harkokin Asiya, na kwamitin tsaron kasa a Fadar White House ta kasar Amurka Evan Medeiros, ya ce Amurka ba ta da burin ganin kasar Sin ta samu koma baya a fannin bunkasuwar ta.
Ziyarar aikin da shugaba Barack Obama na kasar Amurka zai kai daga ranar 22 ga watan nan a kasashen Japan da Korea ta Kudu, da Malaysiya, da Philippines, wadanda ke arewa maso gabashi, da kudu maso gabashin Asiya, da ma Japan wadda ke da takaddama da Sin dangane da yankin kasa, ya sa wasu ke ganin Obama na da burin hana bunkasuwar kasar Sin ta samu koma baya.
Game da haka, Mista Evan Medeiros ya bayyana cewa, ga kasar Amurka, abu ne maras ma'ana a yi kokarin hana bunkasuwar kasar Sin. Ya ce yawan kudaden cinikayya tsakanin kasashen biyu, sun kai dalar Amurka biliyan 500, don haka babu wani dalilin da zai sa Amurka ta yi kokarin dakile bunkasar Sin.
Kaza lika Medeiros ya kara da cewa bangarorin biyu suna da butakar mai da hankali kan moriyarsu bai daya, kasashen biyu suna bukatar kara hadin kai wajen tinkarar kalubaloli da ke kawo barazana ga zaman lafiya, da tsaro da gajiyar kasashen duniya baki daya. Bugu da kari kafuwar sabuwar dangankata a tsakaninsu, ta dangata da yadda suke kara hada kai a fannonin daban daban na magance matsaloli. (Danladi)